Tsāme Daga Bukin Rānekun Tuāwa (#11760)

Rānar haifuwar Bab (aminci ya tabbata a garēshi)
*Da sūnan wanda aka haifa a wannan rāna, wanda Allah ya haliccē shi dōmin ya zama kākākin sūnansa mai īko, mai ƙauna.
Gā allon da muka bayyana a wannan dare da sama da ƙasa suka haskaka da hasken da ya baza ƙyalƙyalinsa bisa duk halitta.
Yā kai wannan dare ! yabo ya tabbata a garēka, sabōda daga garēka nē rānar Ubangiji Allah ta fito, rānar da cikin ƙudirinmu, zā ta zamana fitilar tsīra ga duka mazaunan birānen sūnāye, kuma da ita cē kambun nasarar zakarun dake cikin fagen fāmā na har abada, kuma da ita cē assubāhin murna da zumūɗi ga duk halitta.
Yabo matuƙa ya tabbata ga Allah Ubangiji, mahaliccin sammai, wanda ta garēshi wannan rānā ta ambaci wannan sūna, ta kēcē lābilan zatuttuka na wōfi, ta shūɗē yanannakin tunānin banza, kuma da garēta sūnansa na innanaha, ya bayyana a jiririn hakīka. Ta garēka nē aka būɗē tūlun ruwan rāyuwa har abada, aka būɗē makullin ƙōfōfin sani da na kalma ga idānuwan al’ummōmin dūniya, kuma bazarar Arrahamānu ta būsa a kōwane wajāje. Ɗaukaka ta tabbata ga wannan sā’i da cikinsa nē alfarmar Ubangiji, mai īko, masani, mai hikima ta bayyana !
Yā kē majalasar sama da ƙasa ! Wannan nē daren farkon da Allah ya sō shi da zama alāmar dare na biyu da aka haifi Wanda bābu kirārin da ya isa ya kwatanta matsayinsa. Murna ta tabbata ga wanda ya yi tunāni bisa waɗannan darāre biyu : a gaskiya zai gāne da cēwa, kasancēwarsu da ake gani tā daidaita da tūshensu na ainafi, kuma zai gāne ya fahimta da gaibunan da suke ƙunshe a cikin wannan wahayi, wahayin da ta garēshi nē ginshikan īmānin ƙarya suka rūshe, gumāken camfi suka tarwatse, kuma aka warware tūtar dake furucin cēwa « Bābu wani Allah illā Shī, mai īko, al malīku, mafi kwatanci, mai kārēwa, Al azīzu, da ya fi a kai garēshi ».
A wannan dare nē, ƙamshin turāren kusanta ya bazu, ƙōfōfin haɗuwa a rānēkun ƙarshe suka būɗe warai, kuma duk halitta ta gilgizu tana faɗa cēwa : « Daula ta Allah cē, Ubangijin duka sūnāye, shī da ya zō da mulki na musamman ya mallaki dūniya gabāɗayanta !». Wannan dare, majalasar samāniya tā karrama yabon Ubangijinta, Al’malīku, Maɗaukakin Sarki, kuma gaskiyar sunāyen Allah ta yi yabon Wanda Shīnē sarkin farkō da ƙarshe a wannan wahayi, wanda ƙarfinsa ya sā tsaunika suka zāburo zuwa wajen wanda ya isa ga kōmi da kōwa, mafi ɗaukaka, ya jūya zukācen masōya wajen fuskar masōyinsu, ya sā bazarar ƙauna ta mōtsa ganyāye, cikin murna, muryōyin itāce suka amshi kiran wanda bā shi da iyāka. Duka dūniya ta yi gilgiza cikin bēgen kaiwa ga Sarki madawwami, kuma wannan kalmā ɓōyayyā ta bayyana cikin īkon sūnā, ta maida kōmi ya zama sābo.
Yā kai daren Al’karīmu ! A gaskiya, a garēka muna ganin umul kitābi. Shin, kitābi nē, kō kuma haifaffan ɗā nē ? Āā, nī da kaina nā shaida cēwa ! waɗannan batūtuwa na daular sūnāye nē alhāli kuwa, Allah Ubangiji yā ɗaukaka wannan kitābi sama da duka sūnāye. Ta wannan kitābī nē, gaibu ɓōyeyye da ingantaccen sirri suka bayyana. Nā rantsē da rāyuwāta cēwa, duk abun da aka ambata na daular laƙani nē, alhāli umul kitābi nā sama da duk waɗannan abūbūwa. A garēshi nē alāmun « Bābu wani Allah sai Allah » suka bayyana sama ga kōmi. Nā shaida cēwa, kō da yake kōwa yā san da haka, kamar yanda Ubangijinka ya sanar, kunnansa nē kawai yake iya jin su. Murna ta tabbata ga wanɗanda suka amince da wannan !
Sai cikin māmāki, alƙalamin Mai sama ya yi kira cēwa : « Yā kai wanda kai nē ɗaukakakke sama ga duka sūnāye ! īnā rōƙon ka, don girman īkonka da ya mallaki sama da ƙasa, ka sauke mani nauyin ambatar ka, sabōda nī kaina, nā kasance don īkonka mai rāyāwa. Ta ƙāƙā zan iya kwatanta duka abūbuwan da duk halitta ta kāsa kwatantāwa ? Amā fa, nā rantse da ɗaukakarka, idan na furta ilhāmar da ka sā a raina, duk halitta gabāɗayanta, zā ta mutu don murna da jin dāɗi, abun dake nūna cēwa, a wannan haskekken wuri maɗaukaki wanda ya wuce kōmi, wannan halitta zā ta gamsu gaban tēkun kalmarka. Yā Ubangiji, ka yardēwa wannan alƙalami mai wata-wata, ya dēna kirārin wannan muhimmin matsayi, kuma ka dūbē ni da idon rahama, yā kai Sarkīna Ubangijina. Ka manta da kuskurēna a gabanka. A gaskiya kai nē Ubangijin falalā, Mai īkō, mai gāfartāwa kullun, Al’karīmu.
(Ayyan-i-Tis’ih shāfi 12 zuwa 15)

-Bahá'u'lláh
-----------------------

Tsāme Daga Bukin Rānekun Tuāwa (#11761)

Rānar haifuwar Baha’u’llah (aminci ya tabbata a garēshi)
*Shīnē tsarkakakke, maɗaukaki, Mafi girma
Rānar bukin karramāwa cē, wandan shīnē kyāwon Ubangiji Allah, jabbāru, mai īko, mai ƙauna, yā hau gadon īkonsa. Murnā ta tabbata ga wanda, a wannan rānā ya kai garēshi, kuma wanda Allah, mai cēto cikin matsala, madawwami, ya dūbi wajensa. Ka cē: Mun karrama wannan buki cikin kurkuku mafi girma, a lōkacin da sarākunan dūniya suka tāshi suka yāƙē mu. Ammā fa, ƙarfin azzālumai har abada bā ya iya jā da mu, kuma rundunōnin dūniya har abada bā su iya murƙushe mu. Haka Arrahamānu yake shaidāwa.
Ka cē: ashē yā cancanta a tūre tūshen hakīkantaka gaban sūrūtan al’ummōmin dūniya? Ā’ā, nā rantse da kyāwonsa dake haske duk abūbuwan dā da na gōbe! A gaskiya wannan cē alfarmar Ubangiji da take lulluɓē duk halitta, kuma haka nē īkonsa da ya mallaki duk abūbuwan dake gani da duk abūbuwan da ake gani. Ku riƙe igiyar muhimmin īkonsa, kuma ku ambaci Ubangijinku mai ƴanci, a wannan assubāhi da haske yake gwada duk gaibu ɓōyeyye. Haka nē madawwami ya faɗa a wannan rānā da aka būɗe zāɓeɓɓen ruwa.  Ku yi hattara, kada tunānin shirmen waɗanda suka ƙi yarda da Allah su tāda hankulanku, kō kuma zatuttukansu na wōfi, su nīsantā ku da madaidaiciyar hanya.
Yā kē al’ummar Baha! bisa fukāfukan dangana, ki hira ki shiga cikin sararin ƙaunar Ubangijinki, mai rahama, kuma ki tāshi dōmin ki kai Ubangijinki ga nasara, kamar yanda ādanannun alluna suka ƙadarta. Kada ki yi jāyayya da kōwa cikin bāyūna. Ki mīƙā musu zāƙin tsarkakakkun kalmar Ubangiji, sabōda, da īkonta nē mutāne suke iya sāmun dāmar jūyāwa wajensa. Duk waɗanda a yau, ba su kula da Allah ba, sun ɓata cikin shāwarsu, cikin ba su mā gāne ba. Murna ta tabbata ga wanda, cikin ƙasƙanta da tawāli’u, ya jūya fuskarsa wajen assubāhin āyōyin Ubangijinsa.
Yā cancanta ka tāshi ka karantar da mutāne bisa abun da aka bayyana cikin kitābin Ubangijinsu, mai īkō, mai ƴanci. 
Ka cē: ka ji tsōron Allah, kuma kada ka kula da zatūttukan wōfi da waɗanda suke tafiya bisa hanyar shakka da rishin ādalci suke faɗa. Da zuciya mai armashi, ka jūya wajen fādar Ubangijinka, mamallakin duka sūnāye. A gaskiya, zai taimakē ka da ƙarfin gaskiya. Bābu wani Allah illā Shī, mai īko, mai cikakkiyar kyauta.
Yana yiyuwa ka gaugauta zuwa ga ƙaramin tabki, alhāli gā babban tēku nan gaban idonka? Ka jūyā gabādayanka wajensa, kada ka bi sāwun kōwanne daga cikin kāfirai maƙaryata. Tsuntu madawwami nā wāƙā bisa rassun itāciyarmu ta Ubangiji. Nā rantse da Ubangiji Allah! wāƙarta guda ɗaya tak, tā isa ta shāwar da majalasar samāniya, har mā, mazaunan birānen sūnāye, kuma har mā waɗanda suke zāgayāwa, suna kēwaya gadon mulki sāfe da marēce.
Haka nē, ruwan kalmōmi yake zubōwa daga samāniyar ƙudirin Ubangijinka, mai rahama. Ku jākuɗo kusanta, yā ku al’umma, ku yi wātsi da waɗanda suke gardama ta wōfi da banza bisa āyōyin da Allah ya sauko, kuma da suka ƙi yarda da Ubangijinsu da ya zō musu ɗauke da hujja da shaida.
(Ayyam-i-Tis’ih shāfi 45-47)

-Bahá'u'lláh
-----------------------

Tsāme Daga Bukin Rānekun Tuāwa (#11762)

Rānar haifuwar Baha’u’llah (aminci ya tabbata a garēshi)
*Shīnē tsarkakakke, maɗaukaki, Mafi girma.
Cikin wannan watā nē, aka haifi wanda yake ɗauke da sūnā mafi girma, wanda bayyanarsa ta kāwo gilgiza ga duka al’ummōmin dūniya, wanda ƙūrar sāwunsa ta zama abun yabo ga majalasar samāniya da mazaunan birānen sūnāye. Dōmin wannan haifuwa, sai suka yi gōdiya ga Allah, suka yi gūɗa, kuma suka jī dāɗi matuƙa. Nā rantse da Allah! gā watan da ta garēshi nē duk watanni suka haskaka, watā da cikinsa nē wanda shīnē gaibu ɓōyeyye da ma’ādani tsararre ya bayyana, kuma ya ɗaga muryarsa cikin ƴan adam. Duka īkō nā hannun wannan jinjiri, da ta garēshi nē fuskar halitta ta sāmu hasken murmushi, itāce suka yi līlō, tēkuna suka kumbura, tsaunika suka tāshi, aljanna ta ɗaga murya, dūtsi ya yi kūwa, kuma sū duka suka cē : « Yā ku majalasar halitta ! ku tāshi ku nufi gabashin fuskar Ubangijinku, mai rahama, mai jinƙai ! ».
A cikin wannan watan nē, ita kanta aljanna ta sāmu ado da ƙyalƙyalin fuskar Ubangijinta, mai rahama, sūdar samāniya ta rēra wākarta bisa itāciyar Ubangiji, kuma zukācen gātāye suka ji dāɗi. Sai dai inā, yawancin mutāne ba su kula ba. Murna ta tabbata ga wanda ya yarda da Shi, kuma ya gāne da alkawalin dake cikin kitābin Ubangiji, mai īko, wanda shīnē abun yabo, kuma rūɗāni ya tabbata ga wanda ya jūwa bāya ga wanda majalasar samāniya ta kafa kallonta a garēshi, wanda ya ƙaryatar da kāfirai ɓatattu.
Idan ka sāmu wannan allō, ka wāƙe shi da iyākar zāƙin murya, kuma ka cē : Yā Ubangijīna mai rahama, yabo ya tabbata a garēka, da ka tuna da ni cikin wannan allō wanda ta garēshi ƙamshin rīgar saninka ya fitō, kuma ka malālō tēkunan alfarmarka. Nā shaida da cēwa, kana da īkon yin abun da ka ga dāma. Bābu wani Allah illā kai, mai īko, masanin kōmi da kōwa, mai hikima.
(Ma’idiy-i-Asmani kundi na 4 shāfi 342)

-Bahá'u'lláh
-----------------------

